HUKUMAR HISBAH TA JIHAR KANO TA KAI ZIYARA MASARAUTA KARAYE

A yau Laraba, 3 ga Satumba, 2025, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kai ziyara masarautar Karaye, inda ta gana da Mai Martaba Sarkin Karaye da sauran manyan masu ruwa da tsaki a yankin.

Wannan ziyara ta samu jagorancin Mai Girma Babban Kwamanda na Hisbah, Imam Aminu Ibrahim Daurawa, tare da Mai Girma Chairman na Hukumar, Malam Shehi Shehi Mai Hula, da kuma Mai Girma Babban Darakta, Malam Abba Sa’idu Sufi.

Haka kuma an samu halartar Mukaddasin Babban Kwamanda, Dr Mujahiddeen Aminuddeen, Mataimakiyar Babban Kwamanda, Dr Khadija Sagir Suleiman, tare da sauran Daraktoci da manyan jami’an hukumar.

A yayin wannan ziyara, tawagar ta samu tarba daga Mai Martaba Sarkin Karaye, inda aka tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban masarautar Karaye, da kuma shawarwari kan yadda za a ci gaba da inganta zaman lafiya, kyakkyawan tarbiyya da tsaro a cikin al’umma.

Ziyarar ta kasance mai cike da tarihi da kuma zumunci, wacce ta kara dankon alaka tsakanin hukumar Hisbah da masarautar Karaye.

Abba Ibrahim
Babban mai daukowa gwamnan jihar ka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *